January 15, 2025

Kano: Waɗanda suka mutu a sakamakon wutar da aka cinna wa masallaci sun kai 8

0
IMG-20240515-WA0052.jpg

Mutanen da suka mutu a wutar da ake zargin wani mutum ya cinna wa masallaci a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun ƙaru zuwa takwas, a cewar wani rahoton BBC Hausa.

BBC ta ce da safiyar yau Laraba rundunar ‘yan sandan jihar ta ce ta kama Shafi’u Abubakar mai shekara 38 da ake zargin ya kunna wa masallacin wuta lokacin da mutane fiye da 30 ke sallar Asuba a ciki.

Lamarin ya faru ne a garin Gadan na ƙaramar hukumar Gezawa.

Wani mazaunin ƙauyen mai suna Hamisu Abdullahi ya faɗa wa BBC cewa mutum takwas ne aka tabbatar da mutuwarsu zuwa yammacin yau Laraba.

“Yanzu haka an kawo gawar mutum bakwai da muka yi wa jana’iza, ɗayan kuma sai gobe da safe za a binne shi,” in ji shi yana mai cewa ɗaya daga cikinsu ɗan’uwansa ne.

Ya ƙara da cewa “waɗanda suka rage a asibitin za su kai kamar 22”.

‘Yan sanda sun ce mutumin ya yi amfani da bam ɗin da aka haɗa da man fetur, inda mutum 24 duka maza suka ji raunuka, 20 daga cikinsu manya da kuma yara huɗu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *