May 16, 2025

Kamfanin NNPC Ya Sallami Manyan Jami’ansa

IMG-20250430-WA0003

Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) ya sallami daraktocin gudanarwa na manyan matatun mai uku da ke ƙasar nan, a wani sabon sauyin shugabanci da aka aiwatar a kamfanin.

Rahotanni sun tabbatar da cewa matatun da abin ya shafa sun haɗa da na Warri da Kaduna, inda aka sallami shugabanninsu baki ɗaya.

Haka zalika, wasu manyan jami’an kamfanin da ke rike da muƙamai a sassa daban-daban suma abin ya shafa, ciki har da Bala Wunti, tsohon shugaban reshen kamfanin na NAPIMS.

Bayanin ya kuma nuna cewa NNPC ta umurci ma’aikatan da shekarun su na aiki suka rage kasa da shekara guda su yi ritaya da gaggawa.

Sai dai har zuwa yanzu, babu wata sanarwa ta hukuma da kamfanin ya fitar, amma majiyoyi daga ciki sun tabbatar da wannan sauyi da aka aiwatar.