Kamfanin BUA ya yi wa ma’aikatansa ƙarin kaso 50 cikin 100 na albashinsu
Daga Sabiu Abdullahi
Shugaban Kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya ce kamfanin ya amince da karin albashin ma’aikata da kaso 50 cikin 100.
Rabiu ya bayyana hakan ne a cikin wata takarda ta cikin gida da Mista Mohammed Wali, shugaban ma’aikata na BUA ya sanya wa hannu ranar Lahadi a Legas.
Sanarwar ta ruwaito shugaban BUA na cewa an yi karin kudin ne don rage tasirin matsalolin tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu.
Ya ce karin albashin zai shafi ma’aikata na dindindin da na wucin gadi daga ranar 1 ga Fabrairu, 2024.
“Sabods wannan dalilin, Sashen Ɗaukar Ma’aikata da Kudi suna kokarin aiwatar da karin don tabbatar da cewa an saks shi a cikin albashin watan Fabrairu na 2024.
“Ana fatan da wannan gagarumin karimcin, za mu kara himma wajen gudanar da ayyukanmu tare da yin iya kokarinmu don tabbatar da kwarin gwiwa da ake da shi a kanmu,” in ji shi.