April 19, 2025

Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas, Ya Nuna Goyon Baya Ga Gyare-Gyaren Dokar Haraji

FB_IMG_1734542495795.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce karancin harajin da Najeriya ke samu yana haifar da babban cikas ga ci gaban kasar.

Ya bayyana haka ne a yau Laraba, yayin gabatar da kudirin kasafin kudin 2025 da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a wani taron hadin gwiwa na Majalisar Tarayya a Abuja.

Abbas ya nuna damuwarsa kan yadda rabon haraji zuwa GDP ya tsaya kan kashi 10.9 cikin 100 a 2024, wanda ya ce shi ne mafi ƙaranci a nahiyar Afirka, idan aka kwatanta da matsakaicin kashi 15.6 cikin 100 na sauran Kasashen nahiyar.

Har ila yau, ya ce tara kudin VAT a Najeriya ya tsaya a kashi 20 cikin 100, wanda ya yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da kasashe kamar Afirka ta Kudu da Equatorial Guinea.

Ya jaddada bukatar gaggawar gyara dokokin haraji domin fadada tushen harajin kasar, inganta bin doka, daidaita tsarin gudanarwa, da kuma rage dogaro da bashin kasa da kasa.