May 16, 2025

Kada Ku Bai wa ‘Yan Sanda Rancen da Za Su Gagara Biya—Sufeta Janar na Ƴansanda

images - 2025-04-23T151103.871

Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Dr. Kayode Egbetokun, ya bukaci al’ummar da jami’an tsaro ke aiki a yankunansu da su daina ba su rancen kuɗaɗe masu yawa da za su kasa biya.

Sufetan ya yi wannan kira ne a ranar Talata yayin kaddamar da sabuwar hedikwatar ‘yan sanda da aka gina a gundumar Imane, karamar hukumar Olamaboro a Jihar Kogi.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Miller Dantawaye, ne ya wakilce shi a wurin taron.

“Wasu daga cikin jami’an da za a turo muku aiki da su na iya neman rance ko taimakon kuɗi. Amma ina roƙon ku da kada ku yarda ku ba su bashin da zai gagare su biya,” in ji Dantawaye yayin jawabin sa.

Ya kuma bukaci al’ummar yankin da su kula da sabuwar hedikwatar ‘yan sanda da aka gina, wacce ita ce irinta ta farko a yankin, wacce wani ɗan asalin yankin, Dr. Peter Ali, ya gina tare da bayarwa kyauta don amfanin jama’a.

A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Usman Ododo, ta bakin mataimakinsa Joel Oyibo, ya yaba da wannan kyauta, yana mai ƙarfafa al’umma da su mara wa jami’an tsaro baya domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin.