June 14, 2025

Jirgin Yakin Sojin Najeriya Ya Kashe Mutum Shida Bisa Kuskure a Katsina

images-2025-02-17T112939.829.jpeg

Rahotanni daga jihar Katsina na cewa jirgin yakin sojin Najeriya ya kashe mutum shida bisa kuskure yayin da sojoji ke kokarin fatattakar wasu ‘yan bindiga.

Mazauna kauyen Zakka sun ce jirgin ya jefa bama-bamai kan rukunan bukkoki, lamarin da ya yi sanadin mutuwar fararen hula shida.

Wani rahoto ya bayyana cewa luguden wutar ya biyo bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kan sansanin ‘yan sanda, inda suka kashe jami’ai biyu da wani dan sintiri guda daya.

A halin yanzu, kungiyar Amnesty International ta bukaci a gudanar da bincike kan lamarin, amma rundunar sojin Najeriya ba ta ce uffan ba dangane da wannan hari na kuskure.

Wannan ne karo na goma da ake samun irin wannan hari a cikin shekaru biyu da suka gabata, sannan karo na 11 cikin shekaru takwas.

A baya dai, sojoji sun sha bayyana cewa irin wadannan hare-hare na faruwa bisa kuskure, kuma an dauki matakan rage yawaitarsu.