Jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Abuja ya kauce hanyarsa
Daga Sodiqat Aisha Umar
Rahotanni sun bayyana cewa wani jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya kauce hanya a safiyar wannan Lahadin.
Jirgin wanda ya baro Kaduna ya kauce hanya ne da misalin karfe 9:30 na safiya a daidai yankin Jere da ke Ƙaramar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna.
Bayanai sun ce wannan lamari dai ya katse hanzarin gomman fasinjojin da jirgin ya dauko.
Kawo yanzu dai ana ci gaba da kokarin gyara jirgin wanda kusan taragonsa guda uku suka sauka daga hanya.
Tuni dai jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ’yan sanda suka isa wurin da jirgin ya yi hatsari da ke tsakanin wasu duwatsu.