January 15, 2025

Jihar Yobe ta buƙaci ɗauki daga Bankin Duniya saboda ambaliyar ruwa

0
IMG-20240426-WA0014.jpg

Daga Sodiqat Aisha Umar

Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ya nemi Bankin Duniya da ya kawo musu ɗauki tare da ƙara ƙaimi ga ƙoƙarin gwamnati na samar da hanyoyin magance ambaliyar ruwa da ake sa ran za a fuskanta a wannan damina ta bana.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da harkokin ’yan jaridu na Gwamnan, Mamman Mohammad ya fitar a Damaturu.

A cewarsa, Gwamna Buni ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karɓi tawagar Bankin Duniya da na Shirin Acresal da suka kai masa ziyara.

Gwamna Buni, ya bayyana cewa, matakin da ya fi dacewa don daƙile ambaliyar, shi ne gina magudanan ruwa da za su bi da ruwa a garuruwan da ke da wannan matsala a cikin jihar.

Shugabar tawagar ta Bankin Duniya, Misis Joy Iyanga Agene, ta ba da tabbacin bai wa gwamnatin jihar goyon baya domin ceto al’umma daga ambaliyar ruwa.


Ta kuma yaba wa gwamnatin Jihar Yobe bisa samar da yanayi mai kyau wanda ya inganta ayyukan da shirin na Acresal na Bankin Duniya a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *