January 15, 2025

Japan za ta halarta haɗa magunguna da tabar wiwi

5
image_editor_output_image1040792025-1701943308255.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Kasar Japan ta zartar da wani kudiri na halasta magungunan tabar wiwi a wani gagarumin bitar da ta yi ga tsauraran dokokinta na muggan kwayoyi.

Canje-canje ga dokokin sarrafa cannabis da kwayoyi na Japan da aka zartar a ranar Laraba a zauren majalisa za su ba da damar dage haramcin da aka yi kan kayayyakin kiwon lafiya da aka samu daga tabar wiwi.

Magunguna na tushen tabar wiwi waɗanda aka samar tare da sinadarin cannabidiol, ko CBD, an riga an yi amfani da su a ƙasashen waje don magani a yanayi daban-daban kamar farfaɗiya mai tsanani.

Wannan nasara ce ga kungiyoyin marasa lafiya da suka yi fafutukar neman samun wadannan magunguna.

5 thoughts on “Japan za ta halarta haɗa magunguna da tabar wiwi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *