February 10, 2025

Jam’iyyar APC Ta Kori Tsohon Gwamnan Osun, Rauf Aregbesola

3
images-2025-02-01T152912.706.jpeg

Jam’iyyar APC ta kori tsohon gwamnan jihar Osun kuma tsohon ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, bisa zargin aikata abubuwan da suka saba wa jam’iyya.

Reshen jam’iyyar APC na jihar Osun ne ya tabbatar da korar tasa a cikin wata wasika da ya fitar.

Aregbesola, wanda ya rike mukamin ministan cikin gida a gwamnatin da ta gabata, ya jagoranci wani bangare na jam’iyyar APC a Osun da aka fi sani da The Osun Progressives, wanda daga baya aka sake masa suna zuwa Omoluabi Caucus.

Korar tasa ta biyo bayan wani taro da Omoluabi Caucus ya gudanar a karkashin jagorancinsa, inda bangaren ya bayyana aniyarsa ta ficewa daga jam’iyyar APC, yana mai zargin cewa tasirin jam’iyyar a jihar ya ragu sosai.

3 thoughts on “Jam’iyyar APC Ta Kori Tsohon Gwamnan Osun, Rauf Aregbesola

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *