Jami’ar Alqalam ta tabbatar da sace ɗalibanta mata
![Alqalam-University.jpg](https://tcrhausa.com/wp-content/uploads/2024/01/Alqalam-University.jpg)
Daga Sabiu Abdullahi
Jami’ar Al Qalam, Katsina ta tabbatar da sace wasu dalibanta mata guda biyu.
Jami’ar ta ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin.
Wata sanarwa da shugaban al’amuran jama’a na jami’ar, Akilu A. Atiku, ya fitar, ya bayyana cewa iyayen daliban sun tabbatar da sace su.
Sanarwar da ke kunshe a cikin wata takarda ta musamman ta jami’ar ta ce shugaban jami’ar, Farfesa Nasiru Musa Yauri, yana tare da iyalan daliban yayin da suke cikin wannan mawuyacin hali.
An sace daliban ne a ranar Litinin a kan hanyarsu ta zuwa jihar Katsina daga jihar Neja don ci gaba da gudanar da ayyukan karatunu a jami’ar.