Jami’an Tsaro Sun Kashe Fitaccen Ɗan Ta’adda Ɗan-Isuhu a Zamfara

Rahotanni daga Jihar Zamfara na nuna cewa jami’an tsaro sun kashe wani fitaccen ɗan ta’adda mai suna Ɗan-Isuhu, wanda aka ce ya addabi yankunan Tsafe da Ɗansadau, tare da hana walwala a babbar hanyar Funtua zuwa Gusau.
Wannan labari ya fito ne daga wani rubutu da Abdul Aziz Abdula Aziz, wani mai taimaka wa Shugaban Ƙasa, ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Alhamis.
A cewarsa, jami’an tsaron sun samu galaba a kan Ɗan-Isuhu, wanda ya yi ƙaurin suna a aikata ta’addanci a yankin.
Mutanen yankin sun dade suna kokawa kan ayyukan ‘yan ta’adda a Zamfara, musamman a kan titunan da ke da muhimmanci ga harkokin sufuri da kasuwanci.
Wannan ci gaban na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke ƙoƙarin daƙile matsalar tsaro a arewacin Najeriya.
Duk da wannan nasara, ana ci gaba da kira ga hukumomin tsaro da su ƙara kaimi wajen murƙushe sauran gungun ‘yan ta’adda da ke ci gaba da tayar da zaune tsaye a yankin.