January 15, 2025

Jami’an tsaro sun kama wasu da ake zargin suna da alaƙa da Bello Turji a Sokoto  

0
FB_IMG_1724586032316

Daga Sabiu Abdullahi  

Akalla mayaka 18 da ke da alaka da fitaccen shugaban ‘yan ta’adda Bello Turji aka kama a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya.  

Jami’an tsaron Najeriya ne suka kama mutanen a kusa da kan iyakar Najeriya da Nijar, biyo bayan kisan gilla da wasu ‘yan bindiga suka yi wa Hakimin gundumar Isa Muhammad Bawa.  

Wani faifan bidiyo ya nuna ‘yan ta’addan da aka kama suna tsare a wani dandali, ana yi musu ba’a, tare da yi musu tambayoyi daga jami’an tsaro.  

“Na zo muku da sallama, a nan tare da mu akwai ‘yan bindiga, mayakan Bello Turji da muka kama a kan iyakar Najeriya da Nijar,” an ji daya daga cikin jami’an tsaron yana faɗi.  

A cewar Zagazola Makama, wani mai sharhi kan harkokin tsaro kuma kwararre kan yaki da tada kayar baya a yankin tafkin Chadi, an kama mutanen ne a wani samame da jami’an tsaro suka kai kan ‘yan fashi da makami a yankin.  

“Wadanda ake zargin suna da alaka da kungiyoyin da ke dauke da makamai a karkashin jagorancin Bello Turji, wadanda ake alakanta su da yawan hare-hare, garkuwa da mutane, da kuma munanan laifuka a yankin arewa maso yammacin Najeriya,” in ji Makama.

Makama ya bayyana cewa “aikin wani bangare ne na kokarin da hukumomin tsaro ke ci gaba da yi na wargaza hanyoyin sadarwarsu da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *