May 17, 2025

Jami’an tsaro sun damƙe wanda ya yi garkuwa tare da hallaka ɗaliba a Legas

IMG-20240905-WA0022

Daga Abdullahi I. Adam

Rundunar sojin Najeriya ta kama Adeleye Ayomide mai shekaru 23, wanda ake zargi da kashe Idowu Christiana, ɗaliba ‘yar aji na 3 a jami’ar gwamnatin tarayya ta FUNAAB, da ke Abeokuta jihar Ogun.

Domin tabbatar da kamun ne ma rundunar ‘yansandan jihar Legas, a yau Alhamis, ta tabbatar da cewa rundunar sojin ta miƙa mata Ayomide domin cigaba da bincike.

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka yi garkuwa da marigayiyar a kan hanyar Ikorodu zuwa Yaba a jihar Legas a ranar Litinin, 19 ga watan Agusta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kama wanda ake zargin a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X (Twitter) @benHundeyin yau Alhamis.

Kakakin ‘yansandan ya wallafa cewa “Birged na 9 na rundunar sojin ƙasa ya miƙa Ayomide Adeleye mai shekaru 23 ga rundunar’yansanda ta jihar Legas. 

“An yi miƙa shi ne a yau, 5 ga Satumba, da misalin ƙarfe 2 na rana. Ana kuma cigaba da bincike.”

Wannan mummunan lamari dai ya janyo cece-ku-ce a faɗin Najeriya, musamman a shafukan sada zumunta.

‘Yan Najeriya da dama sun yi amfani da shafin Twitter na neman a yi wa Christiana adalci, tare da yin taken #JusticeForChristianah (wato muna neman abi ma Christianah haƙƙinta).

Wani ɗan Najeriya mai suna Man of Letter (#Letter_to_Jack) ya wallafa a shafinsa na Twitter a daren jiya cewa wanda ake zargin yana tsare a bataliya ta 174 ta sojojin Najeriya da ke Ikorodu a jihar Legas.

Ya bayyana yadda aka kama wanda ake zargin cewa, “An fara gudanar da bincike a kan wanda ake zargin ne bayan la’akari da alaƙarsa da Christiana, musamman idan aka lura da yadda suke ma juna tsokaci a shafin Instagram.

“Bayan lura da irin hulɗarsa a Instagram ne, sai jami’an tsaro suka fara bin diddigin ayyukan wayarsa ta salula gami da saƙonnin tes da yake mu’amala da su.

“Bayan tsaurara bincike ne aka cimmasa a gidan iyayensa a wani wuri a Ikorodu. Daga nan ne masuka samu tabbacin kasancewarsa a cikin gidan ta hanyar bin diddigin bayanan wayarsa.

“Nan da nan ne zaratan sojojin Najeriya na bataliya ta 174bn suka kai farmaki kan wanda ake zargin don tabbatar da kama shi.

“Bayan kama shi, an ga shaidu masu muni da ke nuna ya aikata laifin, ciki har da wata shuɗiyar wata ta marigayiyar ƙirar ITEL A56.”