December 7, 2025

Jami’an tsaro miliyan 2 ba za su iya kare mutane sama da miliyan 200 ba—babban hafsan sojin ƙasa

IMG-20240925-WA0076

Daga Abdullahi I. Adam

Babban hafsan sojin ƙasa, Janar Taoreed Lagbaja, a jiya Talata, ya ce ba zai yiwu a ce jami’an tsaro miliyan biyu su iya kare al’umman Najeriya sama da miliyan 200 ba.

Janar Lagbaja ya bayyana haka ne a yayin wani taro na fitattun mutane na shekarar 2024 da aka gudanar a garin Ilorin na jihar Kwara.

Babban hafsan sojin, wanda ya samu wakilcin babban hafsan horar da sojoji wato Sanni Mohammed, ya bayyana yadda sojoji ke dogaro da kayan aiki da ake shigowa da su daga ƙetare saboda raunin masana’antu na cikin gida.

Hafsan sojin ya kuma nuna damuwarsa kan rashin isassun kuɗaɗe ga rundunar sojojin Najeriya, wanda ya ce ya yi matuƙar tasiri ga ayyukan sojojin.

Kamar yadda ya ce: “A ƙasar da ke da mutane sama da miliyan 200, ba zai yiwu a yi tsammanin hukumomin tsaro, kusan miliyan biyu, (ciki har da sojoji sama da 100,000 masu aiki ba dare ba rana) ace za su iya kare ɗaukacin al’umma.

“Muna shigo da sama da kashi 90 cikin 100 na buƙatun sojojinmu,” inji shi, inda ya ƙara da cewa “duk da wasu na yunƙurin samar da kayayyaki na cikin gida, dogaro da ƙasar kan kayan aikin soja na ƙasashen waje na cigaba da yin yawa.

“Neman ci gaban ƙasa tare da tsaron ƙasa abu ne mai tsadar gaske, saboda manufofin na buƙatar maƙudan kuɗaɗe.

“A shekarar 2023, ɗaukacin jami’an tsaro na da kasafin kuɗi kusan dala biliyan 2.8, duk da cewa daga bisani sun sami ƙarin kusan dala biliyan ɗaya. Sai dai ba dukkanin waɗannan kuɗaɗe ba ne aka ba jami’an tsaron.

“Rashin kuɗaɗe yana shafan ayyukan jami’an tsaro, kuma hakan na tasiri kai tsaye ga aikin.”

Da yake jawabi game da rashin isassun jami’an tsaro, Lagbaja ya ce: “miyagu na amfani da rashin isassun ma’aikat da ake fuskanta wajen aikata laifuka. Magance hakan na buƙatar ware isassun kuɗaɗe wajen faɗaɗa tare da da ƙarfafa jami’an tsaro, da tabbatar da isassun ma’aikata da kayan aiki.”

1 thought on “Jami’an tsaro miliyan 2 ba za su iya kare mutane sama da miliyan 200 ba—babban hafsan sojin ƙasa

Comments are closed.