Jami’an NDLEA sun kama wasu mutane ɗauke da makamai a Nasarawa

Daga Sabiu Abdullahi
Kwamandan hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a jihar Nasarawa, Peter Onche-Odaudu, ya sanar da kama wasu mutane biyu da ake zargi a hanyar Keffi-Nasarawa bisa laifin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
An bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a garin Lafia babban birnin jihar a ranar Juma’a.
Onche-Odaudu ya bayyana cewa jami’an hukumar da ke yankin Keffi na hukumar sun gudanar da sintiri na yau da kullum a kan hanyar Keffi zuwa Nasarawa a ranar 28 ga watan Oktoba, 2023, inda suka tare wata motar kasuwanci domin gudanar da bincike.
A yayin binciken an kama wasu mutane biyu Abdulrahman Sani mai shekaru 20 da kuma Ibrahim Usman mai shekaru 20 a kan hanyar zuwa Nasarawa-Toto.
An same su da bindigar da aka kera a cikin gida da harsashi daya, a boye a cikin bakar jaka,” inji shi.
Kwamandan jihar ya ci gaba da cewa wadanda ake zargin sun karbi bindigar ne daga hannun wani mutum mai suna Sani da ke Tashan Yaro a jihar Katsina, tare da bayar da umarnin kai wa wani Babangida da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a jihar Nasarawa.
Peter ya ce za a mika wadanda ake zargin ga hukumar ‘yan sanda domin gudanar da bincike tare da daukar matakin da ya dace.
“Don tallafawa wannan hadin gwiwa tsakanin hukumomin, alal misali, tsakanin 2022 zuwa 2023 kadai, a kalla mutane hudu an mika su ga rundunar ‘yan sandan Najeriya,” in ji shi.