Jami’an NAHCON sun musanta zargin rashin isasshen abinci ga mahajjata

Daga Abdullahi I. Adam
Zargin da wasu masu amfani da kafafen sada zumunta ke ci gaba da yaɗawa na cewa hukumar kula da aikin hajji ta ƙasa NAHCON na ba wa mahajjatan Najeriya abinci wanda ba ya isarsu ba gaskiya ba ne, inji wata jami’ar hukumar mai suna Malama Fatima Mustapha.
Kamar yadda wasu masu amfani da kafafen sada zumunta suka yi zargi, mahajjatan Najeriya na samun abin kari wanda kwata-kwata wani ɗan kunu ne da wasu ƙananan ƙosai guda uku, sannan sun ƙara da zargin cewa tuni wasu mahajjatan suka fara barar abinci da kuɗi kasancewar hukumar ta gaza ba su ragowar $300 daga kuɗaɗensu na guzuri har yanzu.
Sai dai a martanin da Malama Fatiman ta yi wanda ta wallafa a shafinta na Facebook, jami’ar hukumar ta ƙaryata waɗannan zarge-zarge inda ta saka hoton abincin da ake ba wa mahajjatan wanda ya ƙunshi biredi manya guda biyu, kofin shayi, kunu da kuma kosai haɗe da roba guda ta ruwa.
Daga ƙarshe jami’ar hukumar ta buƙaci jama’a da su yi watsi da waɗancan zarge-zarge domin ba su da tushe balle makama.

Продамус промокод Продамус промокод .
промокод на подключение платежного модуля геткурс platezhnyj-modul-getkurs-promokod.ru .
Heyaa i am forr the primary time here. I camme
across thbis board and I inn finding It really usefful & it helped me out much.
I am hoping tto give oone thing baqck and aidd others sjch aas
yoou helped me.