April 19, 2025

Jagororin APC na Jin Kamar Gwamnatin Tinubu Ta Jefa Su A Kwandon Shara—Inji Sanata Ndume

0
images - 2025-04-12T132922.122

Sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Yamma, ya bayyana damuwa kan yadda wasu manyan shugabannin jam’iyyar APC ke jin kamar gwamnati ta ware su, yana mai cewa rashin jin daɗi na ƙara yaduwa a cikin jam’iyyar tun bayan da Bola Ahmed Tinubu ya hau mulki.

Ndume ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma’a.

Sanatan ya nuna bacin ransa kan yadda wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar ke ganin ba a ba su dama ko haɗin kai daga fadar shugaban ƙasa.

“Tun bayan da gwamnatin ta fara, shekaru biyu ke nan, amma mutane da yawa na kukan cewa an yi watsi da su. Kamar El-Rufai — wanda yanzu ya koma SDP — ya fadi cewa jam’iyyar APC ta manta da shi. Haka kuma akwai wasu da dama da ke cikin irin wannan hali,” inji Ndume.

Ya kuma nuna rashin jin daɗinsa kan yadda fadar shugaban ƙasa ke nuna rashin kulawa ga koke-koken da magoya bayan jam’iyyar ke yi, yana mai cewa hakan na iya janyo koma baya ga jam’iyyar idan ba a gyara ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *