January 24, 2025

Isra’ila tana ƙara zafafa kai hare-hare a Zirin Gaza

4
im-875632-1024x576.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Dakarun tsaron Isra’ila, IDF a ranar Juma’a sun sanar da cewa suna zafafa hare-hare a zirin Gaza don cika burinta a yaƙi da Hamas.

Wannan ya zo ne a yayin da Isra’ila ke ci gaba da zaƙewa wajen kai munanan hare-hare a zirin Gaza.

Da sanyin safiyar Juma’a, sojojin Isra’ila sun kai hari na dare na biyu a arewacin Gaza, bayan sun sha alwashin ci gaba da kai hare-hare ta kasa a cikin kwanaki masu zuwa

Hukumomi na ci gaba da nuna damuwa game da yanayin jin ƙai da kuma makomar fararen hula a yankin.

Ana kara matsin lamba kan ƙasashen duniya don shawo kan Isra’ila ta ba da damar kai kayan agajin da ake bukata a Gaza.

Yayin da aka kai kayan agajin na farko sun samar da abinci, ruwa da magunguna, ba a haɗa da man fetur ba, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta ce ya gurgunta ayyukanta.

Isra’ila ta ce Hamas na tara mai domin amfanin kanta, ta kuma yi kira ga kungiyar Falasdinawa masu fafutuka da ke mulkin Gaza da ta raba a yi amfani da shi.

4 thoughts on “Isra’ila tana ƙara zafafa kai hare-hare a Zirin Gaza

  1. I wass suggested thks website bby myy cousin. I’m not sure whether this post iis
    written bby him aas nobody else know such etailed aboout mmy problem.
    Youu aare wonderful! Thanks!

  2. I am not certain where you’re gettfing your information, buut grat topic.
    I must spen somje tme learning mufh mire orr working out more.
    Thnks foor wondeeful info I was searchhing for this info ffor my
    mission.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *