November 8, 2025

Isra’ila ta kashe mutane da dama a Gaza, ciki har da fararen hula, da ƴan gudun hijira 

66a530733036b.image_

 Daga Sabiu Abdullahi  

Wani mummunan harin da Isra’ila ta kai kan wani tanti da ke cikin harabar asibitin Al-Aqsa da ke tsakiyar Gaza, ya yi sanadin mutuwar mutane 5 tare da jikkata wasu 18, a cewar jami’an kiwon lafiya na Gaza.

Harin ya haifar da wata gagarumar gobara, lamarin da ya jefa rayuka da dama cikin hadari a yankin da ke da yawan jama’a.  

Kamfanin dillancin labaran Reuters, kamar yadda ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Falasdinu WAFA, ya ce a wani harin da Isra’ila ta kai kan wasu makarantu biyu da ke kusa da birnin Gaza, akalla Falasdinawa 25 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata.  

Sojojin Isra’ila sun yi ikirarin kai harin ne kan wani mayaƙi da ke da hannu dumu-dumu a “ayyukan ta’addanci” kuma fashewar bam na biyu na nuna cewa akwai makamai a yankin.