Isra’ila Ta Kama Hamdan Ballal, Ɗan Falasɗinu Mai Lambar Yabo ta Nobel

Sojojin Isra’ila sun kama Hamdan Ballal, ɗan Falasɗinu mai lambar yabo ta Nobel, a gaɓar yamma da kogin Jordan bayan wata arangama da ta ɓarke tsakanin Falasɗinawa da Yahudawa ƴan kama wuri zauna, a cewar masu fafutuka.
A cewar rahotanni, ƴan kama wuri zaunan sun kewaye gidan Ballal da ke ƙauyen Susya a wani hari da suka kai a ranar Litinin.
Wani ɗan fafutuka daga Yahudawan Amurka ya bayyana cewa sojojin Isra’ila sun yi wa Ballal duka kafin su ɗauke shi a motar ɗaukar marasa lafiya.
Ballal yana daga cikin daraktoci huɗu da suka shirya fim ɗin No Other Land, kamar yadda ɗaya daga cikin daraktocin fim ɗin, Yuval Abraham, ya tabbatar. Sai dai sojojin Isra’ila sun musanta hakan.
Masu fafutuka sun ce gwamman sojojin Isra’ila da suka rufe fuskokinsu sun kai hari ƙauyen da misalin ƙarfe shida na yamma agogon ƙasar.
Haka zalika, ƴan kama wuri zaunan sun far wa masu fafutuka da sanduna tare da fasa gilashin motarsu, har sai da sojojin Isra’ila suka shiga tsakani.
Ma’aikatar tsaron Isra’ila ba ta ambaci sunan Ballal ba, amma ta sanar da cafke wasu Falasɗinawa uku bisa zargin su da jifan sojoji da duwatsu.