January 15, 2025

Isra’ila ta kai hari sansanin gudun hijirar Falasɗinawa

244
FB_IMG_1698036566675.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Wani bala’i ya afku a sansanin ‘yan gudun hijira na Jenin da ke gabar yammacin kogin Jordan yayin da wani jirgin leken asiri na Isra’ila ya kaddamar da wani mummunan hari.

Harin ya yi sanadin rasa rayukan Falasdinawa uku tare da jikkata wasu fiye da 20, wasu kuma munanan raunuka, kamar yadda majiyoyin tsaro da likitocin Falasdinu suka bayyana.

Wissam Bakr, Daraktan Asibitin Gwamnati na Jenin, ya tabbatar da asarar rayuka, yana mai cewa, “An kai gawarwakin wasu matasa uku, tare da jikkata 20, wasu kuma masu tsanani, zuwa asibitin Jenin sakamakon harin da wani jirgin leken asiri na Isra’ila ya kai.”

Shaidun gani da ido sun ba da rahoton cewa dakaru masu yawa na Isra’ila sun sauka a Jenin, kusa da sansanin, da kuma garin Burqin.

An yi artabu da makamai tsakanin mayakan Falasdinawa da sojojin Isra’ila, lamarin da ya kara tada jijiyoyin wuya a yankin.

Lamarin dai ya faru ne da wani gagarumin abin fashewa da aka yi a kusa da makabartar sansanin, sakamakon wani makami mai linzami da aka harba daga jirgin na Isra’ila na leken asiri.

Hakan dai ya janyo asarar rayukan matasa da dama tare da jikkata wasu da dama.

244 thoughts on “Isra’ila ta kai hari sansanin gudun hijirar Falasɗinawa

  1. вывод из запоя в наркологическом стационаре [url=www.ukroenergo.ukrbb.net/viewtopic.php?f=13&t=21387/]вывод из запоя в наркологическом стационаре[/url] .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *