January 14, 2025

Isra’ila ta kai hari a Siriya a matsayin martani

0
images-2023-11-10T140530.068.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Rundunar sojin Isra’ila a ranar Juma’a ta ce ta kai hari a wani wuri da ke Siriya a matsayin martani ga harin da jirgi ya kai.

Wannan dai na zuwa ne a matsayin martani ga harin da aka kai kan wani ginin makaranta a birnin Eilat da ke kudancin Isra’ila a jiya.

“Ba da jimawa ba, IDF ta kai hari kan kungiyar a Siriya wacce ta kai harin UAV zuwa Eilat Alhamis (jiya).

“Rundunar UAV wacce ta afka wa wata makaranta a cikin garin,” in ji Rundunar Tsaro ta Isra’ila (IDF), a safiyar ranar Juma’a.

A yammacin ranar alhamis hukumar ta IDF ta ce tana nazarin cikakken bayani game da al’amarin lamarin.

Ya zuwa yanzu dai, babu wani rahoton hasarar rayuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *