January 15, 2025

Isra’ila na ci gaba da luguden wuta a Gaza duk da cewa an fara Ramadan

0
FB_IMG_1710151575495.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Mutane a ƙasar Falasɗinu sun fara azumin Ramadan cikin yanayi marar kyau inda ake ci gaba da gwabza faɗa a yankin tsakanin dakarun Isra’ila da sojojin Hamas kuma babu wata alamar cewa za a cimma tsagaita wuta.

BBC Hausa ta rawaito cewa Isra’ila ta ragargaza wuraren zaman mutanen Gaza.

A daidai wannan lokacin ne kuma hukumomin bayar da agaji ke gargaɗin cewa mutane za su mutu saboda matsananciyar yunwa.

A daren da ya gabata an yi artabu bayan da ƴansandan Isra’ila suka hana ɗarurtuwan matasa Falasɗinawa shiga masallacin Al Aqsa.

Shi kuma Benjamin Netanyahu, watau Firaministan Isra’ila, ya na kan bakarsa ta ci gaba da luguden wuta a birnin Rafah da ke kudancin Gaza.

Babu alama Natenyahu zai fasa kudirinsa duk kuwa da cewa Shugaban Amurka Joe Biden ya yi gargadi kan batun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *