Isra’ila da Falasɗinu: Jordan ta jaddada goyon bayanta ga Hamaz
Sarki Abdallah na biyu na kasar Jordan ya bayyana goyon bayansa ga Falasɗinu, yana mai cewa zaman lafiya ba zai yiwu ba a yankin Gabas ta Tsakiya matukar ba a samu ‘yantacciyar kasar Falasdinu ba.
Shugaban na Jordan ya yi magana ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin Isra’ila da Hamas, kungiyar gwagwarmaya a Falasɗinu.
Kungiyar Hamas da ke iko da Gaza ta kaddamar da wani gagarumin hari kan Isra’ila, inda ta kashe mutane akalla 1,200 tare da yin garkuwa da wasu kusan 150 a karshen mako.
Harin ramuwar gayya da sojojin Isra’ila suka kai a zirin Gaza kuma ya yi sanadin mutuwar mutane aƙalla 900.
Da yake jawabi ga wakilai a jawabin buɗe sabon zaman majalisar a ranar Laraba, Sarkin na Jordan ya ce, “Yankinmu ba zai taɓa samun tsaro ko kwanciyar hankali ba tare da samar da cikakken zaman lafiya da kwanciyar hankali ba.”