April 26, 2025

Israa’eela ta ƙona FaIasxināwa 4 da ransu a harin da ta kai wa ƴan gudun hijira

FB_IMG_1728472326464.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Isra’ila ta kashe Falasɗinawa huɗu—ta hanyar ƙona su—tare da jikkata fiye da mutane 40 a wani hari da ta kai wa tantunan da fararen hula suka tsere a cikinsu a Gaza, in ji rahotanni daga kafofin watsa labarai na yankin.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu, WAFA, gobara ta tashi a tantunan da ke kusa da Asibitin al-Aqsa Martyrs a birnin Deir al-Balah, sakamakon harin.

Hotuna da bidiyoyi da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna mutane sun makale cikin tantunan yayin da hayaƙi ya turnuƙe su.

2 thoughts on “Israa’eela ta ƙona FaIasxināwa 4 da ransu a harin da ta kai wa ƴan gudun hijira

Comments are closed.