December 7, 2025

Iska Ta Lalata Gidaje Da Makarantu a Kwara

images - 2025-04-01T074056.128

A kalla gidaje da makarantu sama da 200 ne suka lalace sakamakon gagarumar guguwar iska da aka tafka a Ilorin da Ogele/Eyenkorin da ke karamar hukumar Asa ta jihar Kwara a ranar Lahadi.

Guguwar, wacce aka samu tare da ruwan sama mai karfi, ta kuma kifar da sandunan wutar lantarki, lamarin da ya jefa wasu yankuna da dama cikin duhu.

Rahotanni sun bayyana cewa gine-gine da dama, ciki har da makarantu, shaguna, da wuraren kasuwanci, sun rushe sakamakon karfin iskar.

A yankin Ilorin West, guguwar ta jefa tarkace a cikin magudanar ruwa a gadar Kuntu, wanda ya kara dagula halin da ake ciki.

Wasu daga cikin yankunan da suka fi fuskantar barnar sun hada da Eyenkorin, Ogele, Ifelodun, Ifesowapo, Orisunbare, Odo-Akuo, Apata Ajele, Alagbado Eyenkorin, Basa, Yakoyo, da Lekki.

Daga cikin makarantu da abin ya shafa sun hada da Ogele Primary School, Ansarul-Deen Primary School, da D-Light A-Nur Nursery/Primary School, wadanda rufinsu ya yage gaba daya.

Haka kuma makarantu masu zaman kansu kusan 15 sun samu lalacewa mai yawa, ciki har da Community Secondary School, Apata Ajele, da Wilson School, Alagbado, inda wasu azuzuwa suka rushe.Guguwar ta kuma cire rufin Government Day Secondary School tare da lalata kayan wasan baseball a Adeta da ke Ilorin West.