January 24, 2025

INEC ta ɗage tattara sakamakon zaɓen gwamnan Bayelsa zuwa gobe Litinin

0
images-2023-11-12T204205.828.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yanke shawarar dage tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Bayelsa.

Shugaban sashen wayar da kan jama’a da wayar da kan masu kada kuri’a a ofishin INEC da ke Yenagoa, Mista Wilfred Ifogah, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a cibiyar tattara sakamakon zabe ta jihar.

Tun da farko malamin zaɓe na jihar Farfesa Kuta Farouq ya dakatar da aikin na wani dan lokaci har zuwa karfe 6 na yamma biyo bayan tattara sakamako daga kananan hukumomin Sagbama, Nembe, da Ekeremor.

Jinkirin ya samo asali ne sakamakon hasashen samun sakamako daga sauran kananan hukumomin biyu da suka rage wato Brass da Kudancin Ijaw, wadanda har yanzu ba a kawo su ba har ya kai ga ɗage zaman.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *