“Ina da burin rubuta littafai masu yawa da amfani ga al’umma”—Hajaarah Muhammad Bashar
Jama’a , Assalamu alaikum!
Barkanmu da sake saduwa a cikin filinmu mai farin jini na Fitattun Matasa, wanda fili ne da ke gayyato fitattu kuma jajirtattun matasa da suka taka wani mataki tare da samun nasara a rayuwarsu.
A yau, filin ya samu nasarar gayyato muku wata fitacciyar marubuciya, wacce ta ƙware wajen rubuta littattafai cikin harshen Turanci, wato Hajaarah Muhammad Bashar.
Tana ɗaya daga cikin gwarazan matan da gidauniyar bunƙasa adabi ta Open Arts ta zaɓa domin ɗaukar nauyi buga littattafansu.
Sai ku biyo mu sannu a hankali domin karanta cikakkiyar tattaunawarmu da ita.
TCR: Da farko za mu so jin takaitaccen tarihinki.
Hajaarah: Ni sunana Hajarah Muhammad Bashar. An haife ni a shekarar 1995, a garin Minna na Jihar Neja.
Na kammala digiri ɗina a Jami’ar Alhikmah ta Ilorin a inda na karanta Microbiology. Yanzu haka ina karatun digiri na biyu wato Master’s a Federal University of Technology Minna a fannin Medical microbiology.
Shekaru hudu ke nan da na fara rubutun littattafai ta ɓangaren Turanci.
TCR: Me ya ja hankalinki kika ɗauki ɗauki kwas ɗin Microbiology a jami’a?
Hajaarah: Lokacin da nake sakandire, biology ne na fi so fiye da sauran. Sannan ina ɓangaren kimiyya. Da na gama sakandiren, sai na ga microbiology ne ya fi cancanta na karanta. Ra’ayi ne kawai, ban yi wani zurfin tunani a kai ba.
TCR: Ko mene ne burinki a rayuwa?
Hajaarah: Toh dai ina da abubuwa da yawa da nake so in cim ma. A shafin rubutu, ina burin na ga na rubuta littattafai masu yawa wadanda za su amfani al’umma baki ɗaya. Duk da da Turanci nake rubutawa, ina sa ran zan juya su zuwa Hausa ma—waɗanda ba su iya karatun Turanci ba ma na san za su amfana da takardun.
Sa’annan ina da ra’ayin buɗe NGO nan gaba da zai taimaka wa mutane masu ƙwazo da basira waɗanda ba su da inda za su nuna iyawarsu.
Ta fannin kimiyya kuma, zan so idan na kammala master’s ɗina na fara research a kan cututtuka da kuma yadda za a warkar da su in Allah ya yarda ya kuma bar mu da rai da lafiya.
TCR: Wani Ƙalubalen kike fuskanta kasancewarki marubuciya?
Hajaarah: Kalubalen da nake fuskanta kasancewata marubuciya ya kasance a shafin ƙirƙiro labarai da za su yi fice sannan su kasance daban daga sauran jerin labarai na duniya.
A kodayaushe ina ƙoƙarin gina murya daban waddaa za ta kasance muryata ta rubutu. Wannan abu ya kan ci mun tuwo a kwarya ya kuma tashe ni tsaye wajan ganin na cimma burina.
TCR: Sannan wasu nasarori kika samu a wannan fage?
Hajaarah: Na samu nasarori fiye da zato. Ƙwazo da hazaka da nasa a fagen rubutu ya taimaka min wajan lashe gasa daban-daban a cikin Najeriya da kuma ƙasashen waje. Haka zalika ya taimaka min wajen gano muryar da ta cancanta in yi amfani da ita wajan rubutu.
An buga labaraina a kasashe kamar Najeriya, Ghana, Kenya, Amurka, da sauransu. Na lashe gasa fiye da bakwai da labaraina.
TCR: Kamar wasu nasarori za ki iya bugan ƙirjin kin samu yanzu haka?
Hajaarah: To dai gaskiya suna da yawa. Amman wanda nafi alfahari da shi, shi ne babban gasar da na lashe wanda ake kira The Nigerian Prize for Indigenous Language wanda shi ne daya daga cikin manyan gasar da ke Najeriya. Sannan ina alfahari da nasarar da na samu a cikin wannan watan da aka zaɓe ni daya daga cikin matan Arewacin Najeriya waɗanda za a buga littattafansu nan gaba.
Wannan shi ne babban littafina wanda ya kai shekara takwas tun rubutawa. Fitowata cikin jerin sunayen marubutan ta tabbatar min da cewa wannan littafin ya samu karɓuwa kuma ya cancanci rubutu.
TCR: Rubutunki akan me ya fi mayar da hankali?
Hajaarah: Rubutuna ya fi mayar da hankali kan sha’anin rayuwar duniya da yanayin zamantakewa. Ina kokarin haɗa rayuwar yau da kullum a cikin ƙagaggun labarai na.
TCR: Kenan yanzu mafi yawan kaso na burinki a rubutu ya cika?
Hajaarah: Tabbas rabin burina na rubutu ya cika. Sabida buga wannan babban littafin nawa shi ne burina na farko kasancewa na riga na buga gajerun labaraina da yawa a ko’ina. Ina burin ajiye littattafai sama da goma a doran kasa kafin barina duniya in Allah ya yarda. Kamar yadda Hausawa sukan ce na farko shi ne mai wuya.
Bayan shi kuwa sauran mai sauki ne. Na yarda da cewa bayan an buga wannan littafin, sauran littatafaina da na rubuta na ajiye za su fito suma. Da sannu sannu zan tashi.
TCR: Littattafai nawa kika karanta?
Hajaarah: Lol 😍 Ba zan iya lissafa littattafan da na karanta ba. Sun zarce a kirga su. Tun ina karanta littattafan Hausa har na koma na Turanci. A gaskiya littattafan da suka fi daukar hankalina sune wadanda aka rubuta musamman akan rayuwarmu ta yau. Ina nufin a kan wannan zamanin namu da kuma abubuwan da ke wakana. Ina son na ga an cigaba da ɓullo da matsololin da ke ci mana tuwo a kwarya.
Ba kamar yadda yawancin littattafan Hausa suka maƙe wa soyayya ba. Ba ina nufin su ma ba su da nasu amfanin ba ne. A’a, illa dai ya kamata su jawo wani bangaren da zasu iya taimakon al’umma da yawa.
TCR: Wane marubuci/marubuciya kika fi so?
Hajaarah: Suna da yawa sosai. Ina son rubutun Khaled Hosseini da kuma Abubakar Adam Ibrahim da dai sauransu.
TCR: Wane nau’in abincin Hausawa kika fi so?
Hajaarah: Ɗanwake. Lol. Ba na gajiya da cin ɗanwake. Kuma da yake uwar mahaifiyata ƴar Katsina ce, duk yawancin cimar Hausawa na sansu. Daga shi sai dambu, alkubus da miyar taushe. Ga dai su nan birjik. Abubuwan da nake son ci su suka fi ba ni sha’awa. Sai gurasa. 😁
TCR: Mene ne saƙonki na karshe?
Hajaarah: Saƙona na ƙarshe ga duk mai karanta wannan tattaunawar shi ne yin ƙoƙari da tashi tsaye wajan neman na-kai da ilimi wanda zai amfane ku nan gaba. Rayuwa ba ta da tabbas.
Dole a cigaba da ƙoƙartawa wajan nema, samu da gamawa da duniya lafiya. Kowa na da yancin nema da samun zaman lafiya. A ci gaba da karatu. Littafai da dama suna da hanyoyin bullo wa matsaloli masu yawa. Zasu taimaka maku sosai. Sannan a Turance zan ce “Dream and accomplish. You have the right to dream and be happy.”





Арматура диаметром 32 мм, изготовленная из стали марки А500С, является одним из самых востребованных видов металлопроката в строительстве. Она применяется при возведении фундаментов, армировании стен и перемычек. https://armatura32.ru
For the reason that the admin of this site is working, no uncertainty very quickly it will be renowned, due to its quality contents.
Ridiculous quyest there. Whhat happened after? Goodd luck!
Pretty! This has been a really wonderful post. Many thanks for providing these details.