April 18, 2025

Hukumar ‘Yan Sanda Ta Fara Tantance Masu Neman Aiki, Wannan Karon Ba Sai An Cike Fom Ba

images-2025-02-24T110616.939.jpeg

Hukumar Kula da Aikin ‘Yan Sanda ta Kasa (Police Service Commission) tare da hadin gwiwar Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, ta sanar da fara tantance wasu daga cikin wadanda suka nemi aikin ‘yan sanda a baya.

A cewar sanarwar da hukumar ta fitar, wannan daukar aiki ba zai bukaci sake cike takardar neman aiki ba saboda karancin lokaci.

Za a dauki sabbin kuratan ‘yan sanda ne daga cikin wadanda suka riga suka nemi aikim kuma suka rubuta jarabawar Computer-Based Test (CBT) a ranar 5 da 6 ga watan Maris, 2024, amma ba su samu nasarar shiga aikin ba.

Hukumar ta bukaci wadanda suka cancanta da su duba sunayensu a shafin yanar gizo na hukumar:
👉 https://apply.policerecruitment.gov.ng

Duk wanda ya ga sunansa zai iya buga takardar gayyata (invitation slip) domin halartar gwajin lafiya (medical screening) da za a gudanar a Police Hospitals dake Zonal Headquarters guda 17 a fadin Najeriya.

Za a fara gwajin lafiya daga ranar 26 ga Fabrairu, 2025, sannan a kammala zuwa 12 ga Maris, 2025. Duk wanda bai samu damar yin gwajin ba a wannan lokaci, to ba zai ci gaba da matakin daukar aikin ba.

Hukumar ta bukaci jama’a su yada wannan bayani domin ‘yan uwa musamman mazauna karkara su samu labari.

1 thought on “Hukumar ‘Yan Sanda Ta Fara Tantance Masu Neman Aiki, Wannan Karon Ba Sai An Cike Fom Ba

  1. Understanding the dynamics of Iraq’s economy is crucial, and Iraq Business News offers timely updates on sectors such as oil, agriculture, and construction. Their reporting equips businesses with the knowledge needed to make informed decisions in this rapidly changing environment.

Comments are closed.