January 15, 2025

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta kama manyan jami’ai kan badaƙalar sayen magani

0
images (8) (11)

Daga Sabiu Abdullahi  

Hukumar jin korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta kama wasu mutane biyar da suka hada da manyan jami’an gwamnati bisa zargin badakalar samar da magunguna na biliyoyin naira.  

Wadanda aka kama sun hada da Mohammed Kabawa, babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu; Abdullahi Bashir, shugaban kungiyar Kananan Hukumomin Najeriya (ALGON) reshen jihar kuma shugaban karamar hukumar Tarauni; da Musa Kwankwaso, Manajan Darakta na Novomed Pharmaceuticals kuma ƙane ga jagoran NNPP na kasa, Rabi’u Kwankwaso.  

Ana zarginsu ne da haɗa baki wajen bai wa Novomed kwangilar samar da magunguna ga kananan hukumomi 38 na jihar, wanda hakan ya saba wa dokokin sayan kayayyakin gwamnati.  

Binciken farko ya nuna cewa kowacce daga cikin kananan hukumomin 38 sun biya Novomed Naira miliyan 9.150 domin siyan magunguna, amma har yanzu ba a kawo musu magungunan ba.  

A cewar wata majiya da ke da masaniya kan al’amarin, “Muna da kananan hukumomi 44 a jihar kuma sun yi nasarar karɓar naira miliyan 9.150 daga ƙananan hukumomi 38 domin samar da magungunan da har yanzu ba a samar ba.” 

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Kabiru Kabiru ya tabbatar da kamen, ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike.

“Hukumar na aiki don bankado yadda zamban da ake zargin ta faru tare da gurfanar da wadanda ke da hannu a gaban kuliya,” inji shi.  

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, wadanda ake zargin suna hannun hukumar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *