Hukumar Sharia ta Jihar Bauchi ta shirya taron bita wa Alƙalan majistare kan beli da matakan gyaran hali

Daga Salmanu Isah Darazo
Alƙalan majistare daga jihar Bauchi sun hallara a gandun dajin Yankari don halartar taron ƙara wa juna sani kan beli, wa’adin ɗauri da kuma matakan gyaran hali da hukumar kula da harkokin Shari’a ta shirya.
Taron bitar da ya gudanar jiya, ya tattauna batutuwa da suka shafi hanyoyin rage cunkoso a gidajen gyaran hali da kuma yadda za’a inganta yanke hukunci da Shari’a a faɗin jiha.
Da take bude bitar babbar jojin jiha, me Shari’a Hon. Rabi Talatu Umar da ta samu wakilcin me Shari’a M.A Abubakar ya jaddada bukatar dake akwai ta amfani da sulhu da gargaɗi da kuma ayyukan raya yankuna kamar yadda daftarin horo da laifuka ya tanada.
Me Shari’a Rabi Talatu sai ta jaddada bukatar bada horo kan sana’o’in hannu don dogaro da kai yayin zaman gidan gyaran hali.
Sai ta yabawa hukumar kula da harkokin Shari’a kan shirya bitar kana ta yi kira ga alƙalan da su yi amfani da damar wajen nazartar hanyoyin ladabtarwa maimakon ɗauri.
Taron bitar ya haɗa fitattun masana Shari’a ciki har da me Shari’a M.M Abubakar da me Shari’a Amin Umar I leka na babbar kotun jiha da kuma babban sakataren hukumar Shari’a ta jiha Dakta Ibrahim Danjuma, darktoci da wakilan ma’aikatar Shari’a.
Har wa yau, cikin mahalartan akwai Kompturolan gidajen gyaran hali na jiha, mataimaki Kompturola da jami’an yan sanda.
Ana sa ran taron bitar zai zaburar da alƙalan majistare kan hanyoyin ladabtarwa maimakon ɗauri da kuma sauƙaƙa yanke hukunci don rage cunkoson gidajen gyaran hali da inganta Shari’a a jihar Bauchi.