January 15, 2025

Hukumar Kwastam ta mika wa DSS nakiyoyi 6,240 da aka kama a Jihar Kebbi

0
IMG-20240426-WA0017.jpg

Daga Sodiqat Aisha Umar

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama haramtattun nakiyoyi 6,240 a hanyar Yauri zuwa Jega da ke Jihar Kebbi.

jami’an tsaro hadin gwiwar kwastam, sojoji, ’yan sanda, DSS da kuma hukumar shige da fice ta kasa ne suka kama makama, bayan samun bayanan sirri.

Kwanturolan Kwastam na Jihar Kebbi, Iheanacho Ernest Ojike, ya ce hukumar ta damka wa hukumar tsaro ta DSS wadannan nakiyoyi da aka kama.

Kwanturolan Kwastam na shiyyar ya kara da cewa, an kama nakiyoyin ne a cikin wasu kwalaye 40 da kuma buhuna, wanda suke da matukar hatsari.

Tuni dai aka kama wasu mutane biyu da ke da makaman kuma an gurfanar da su a gaban kuliya, inda alkali ya ba da umarnin tsare su. A cewar Kwanturolan kwastam na jihar kebbi Iheanacho Ernest Ojike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *