Hukumar kwastam a Najeriya ta dakatar da sayar da kayan abinci mai sassauƙan farashi
![1708442373290-750x634.jpg](https://tcrhausa.com/wp-content/uploads/2024/02/1708442373290-750x634-1.jpg)
Daga Sabiu Abdullahi
Hukumar kwastam Najeriya ta dakatar da sayar da kayan abinci da ta fara sayarwa a kan farashi mai sauki.
Abdullahi Maiwada, kakakin hukumar, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
A cewarsa, sun dauki wannan matakin ne sakamakon turmutsitsin da ya yi sanadin salwantar rayuka a hedikwatarta da ke unguwar Yaba a birnin Legas a ranar Juma’ar da ta gabata.
Idan ba a manta ba, a ranar 20 ga Fabrairu, 2024 ne hukumar ta ce za ta sayar da kayan abincin da aka kama a farashi mai sauki
“An fara sayar da kayan abincin a farashi mai rahusa a natse kuma cikin kamala da misalin karfe 0800,” in ji Maiwada, kamar yadda kafar BBC ta ambato shi.
“Mun ji daɗin haɗin kan ɗimbin jama’a da suka haɗa da tsofaffi da nakasassu da mata masu juna biyu, da sauran ’yan Najeriya masu rauni”, inda ya kara da cewa “sayar da kayan abincin ya kasance har zuwa kusan ƙarfe 5 na yamma, kamar yadda sama da masu cin gajiyar 5000 da ‘yan jarida suka tabbatar.”
“Dandazon mutanen sun kasance cikin zaƙuwa inda suka riƙa ture shingayen da muka gindaya domin neman buhunhunan shinkafa wanda aka samu asarar rayuka da jikkata wasu da dama.” In ji Maiwada.