Hukumar EFCC Ta Janye Daga Neman Kama Yahaya Bello
Daga Sodiqat Aisha Umar
Hukumar EFCC ta janye daga neman kama tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello.
Janyewar na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban hukumar, ya sha alwashin sauka daga kujerarsa idan har ba a gurfanar da Yahaya Bello ba
Hukumar ta janye karar da ta daukaka a gaban kotu na neman kama tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello.
Lauyan EFCC, J.S. Okutepa, SAN, ya shaida wa kotun da ke zama a Abuja cewa janyewar ta zama dole saboda sauyawar wasu abubuwa.
Kafin janyewar, EFCC ta daukaka kara ne kan umarnin Babbar Kotun Jihar Kogi da ta hana hukumar kama tsohon gwamnan.
Hukumar ta ce ta mika wa kotu bukatar janye daukaka karar ne saboda lokacin da doka ta kayyade na yin hakan ya riga ya kure.
A ranar 8 ga Afrilu, 2024 Yahaya Bello ya shigar da karar neman kotu ta kare masa hakkokinsa na ɗan’adam, ta hana EFCC yi masa duk wata barazana ko kama shi ko aibata shi ba tare da ba shi takardar gayyata ta hanyar da ta dace ba.
Tsohon gwamnan ya kuma yi zargin cewa akwai wata manufar siyasa a shirin EFCC na kama shi ba bisa ka’ida ba.
A ranar 12 ga Maris EFCC ta daukaka kara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa hujjar cewa kotun farko ba ta da hurumin hana hukumar gudanar da aikinta.
A ranar ce jami’an hukumar suka yi wa gidan tsohon gwamnan da ke Abuja kawanya domin kama shi, bayan sun samu izinin yin hakan daga kotun Abuja.
Sai dai kuma a karshe ba iya kama shi ba, bayan takaddamar da aka samu tsakanin jami’an hukumar da ayarin gwamnan Kogi mai ci, Usman Adodo, wanda ya je gidan.
EFCC na zargin Bello da laifuka 19 da suka danganci safarar kudaden haram, cin amana da facaka da dukiyar gwamnati har naira biliyan N80.2 a zamanin mulkinsa.