January 15, 2025

Hukumar DSS ta kama shugaban NLC Joe Ajaero a filin jirgin sama na Abuja

0
IMG-20240808-WA0011

Daga Sabiu Abdullahi  

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun kama shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja.  

Ajaero dai na shirin shiga jirgi zuwa kasar Ingila domin gudanar da wani aiki ne a lokacin da jami’an DSS suka damƙe shi.  

Majiyoyi sun ce an mika shi ga hukumar leken asiri ta kasa NIA.  

Kungiyar NLC ta tabbatar da kamen, inda ta bayyana shi a matsayin “nuni da rashin tabbas na yadda gwamnatin Najeriya da hukumominta ke ci gaba da yin ta’asa a yunkurinsu na toshe duk wata muryar ‘yan adawa a kasar.”  

Kwanan na ma dai ‘yan sanda sun gayyaci Shugaban NLC kan zargin hada baki, tallafa wa ayyukan ta’addanci, cin amanar kasa, zagon kasa, da kuma aikata laifuka ta yanar gizo.  

Kungiyar kwadago ta NLC ta yi barazanar cewa za ta gudanar da zanga-zanga kan kamun, inda ta bukaci kungiyoyin da ke da alaka da su, da majalisun jihohi, da ma’aikatan Najeriya da su yi taka-tsan-tsan da kuma zama cikin shirin ko-ta-kwana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *