January 15, 2025

Hukuma ta gargadi jama’a game da shagunan yanar gizo masu damfara da sunan Black Friday

18
images-2023-11-24T031208.712.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Yayin da Black Friday ta gabato, Hukumar Kula da Ciniki ta Tarayya (FCCPC) ta ba da sanarwar taka tsantsan game da yuwuwar karuwar shagunan intanet na jabu, tare da leken asirin da ke nuna yiwuwar karuwarsu har zuwa 135%.


Babatunde Irukera, mataimakin shugaban hukumar FCCPC, ya jaddada bukatar yin taka-tsan-tsan, inda ya bayyana cewa, “Akwai mutane marasa kishin kasa da ke cin gajiyar sayayyar ranar Black Friday domin farautar masu saye da sayarwa.”

Irukera ya bukaci masu amfani da su da su keɓance amintattun dandamali na intanet don rage haɗarin fadawa hannun ƴan damfara.

Black Friday dai wata rana ce da aka ware ta a watan Nuwambar kowace shekara don sayar da kayayyaki iri-iri a yanar gizo a kan farashi mai sauƙi.

18 thoughts on “Hukuma ta gargadi jama’a game da shagunan yanar gizo masu damfara da sunan Black Friday

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *