Hope Uzodinma ya lashe zaɓen Imo
Daga Sabiu Abdullahi
An bayyana Hope Uzodimma na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Imo, inda ya samu kuri’u 540,308.
Sanarwar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fitar ta fito ne daga bakin jami’in zaben jihar, Farfesa Abayomi Fasina.
Nasarar Uzodimma ya karade faɗin ƙananan hukumomi 27, wanda hakan ke nufin zai shiga wa’adi mulkinsa na biyu.
Wa’adi na biyun zai fara ne a lokacin da aka yi bikin rantsar da shi a ranar 14 ga Janairu, 2024.