Hisbah ta ƙwace kwalaban giya 850 a Katsina

Daga Sabiu Abdullahi
Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta kama kimanin kwalaben giya iri-iri guda 850 a karamar hukumar Kankara.
Kwamandan hukumar, Aminu Usman, ne ya jagoranci aikin a ranar Lahadi tare da hadin gwiwar jami’an gwamnati.
Rahotanni sun ce an kama barasa da aka kwace a cikin wata mota da kuma hannun masu sayarwa a yankin.
Usman, ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na yakar ayyukan rashin ɗa’a, ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su taimaka wajen gano wuraren da irin wadannan abubuwa ke faruwa.
Ya bukaci jama’a da su marawa hukumar Hisbah baya wajen samar da kyakkyawan yanayin aiki a jihar.