Helikwaftan ma’aikatar sufurin jiragen sama Najeriya ya yi haɗari a Fatakwal
Daga Sabiu Abdullahi
Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya ta Najeriya ta tabbatar da hatsarin jirgin helikwafta da ya faru ranar Alhamis, 24 ga Oktoba 2024.
Jirgin helikwaftan mai suna Sikorsky SK76, mai lambar rijista 5NBQG, wanda kamfanin East Wind Aviation ke aiki da shi, ya fada cikin ruwa a kusa da Bonny Finima a tekun Atlantika da misalin karfe 11:22 na safe.
Wata sanarwa daga ma’aikatar mai dauke da sa hannun shugaban sashen yada labarai, Odutayo Oluseyi, ta ce jirgin yana kan hanya daga sansanin sojoji na Fatakwal zuwa rijiyar mai ta NUIMANTAN, da mutane takwas a ciki.
“An sanar da Hukumar Bincike Kan Hadurran Jiragen Sama ta Najeriya kuma an tura tawagogin bada agajin gaggawa,” inji sanarwar ma’aikatar.
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo (SAN), ya tabbatar da cewa ayyukan ceto da bincike na ci gaba da gudana.