Hayaƙin janareta ya yi ajalin ɗlibai 7 a Bayelsa
Daga Sodiqat Aisha Umar
Kimanin mutum bakwai ne suka n rasa rayukansu bayan shaƙar hayaƙin janareto a wani ɗakin naɗar sauti (studio) a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.
An ce waɗanda suka mutun suna aiki ne a studion, mallakin ɗaya daga cikinsu mai suna Akpos Barakubo, a lokacin da lamarin ya faru a daren ranar Litinin.
A cewar mazauna yankin, ma’aikatan sun yi aiki har tsakar dare, inda suka sanya janareton lantarki saboda rashin wutar lantarki, inda suka yi barci suna aikin.