January 14, 2025

Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya mummunan tashi zuwa 31.7%

0
12375255_0-261-4416-2486.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ƙaru zuwa kashi 31.7% a watan Fabrairu, saɓanin kashi 29.90% da aka gani a Janairu.

Wannan na ƙunshe ne cikin bayanan da suka fito ranar Juma’a daga cibiyar ƙididdiga ta ƙasar, Nigeria’s Bureau of Statistics (NBS).

An ambato sanarwar tana cewa, “Duba da sauyin, hauhawar farashi a Fabrairun 2024 ya nuna ƙaruwar maki kashi 1.80%, idan an kwatanta da Janairun 2024”.

Wani rahoton TRT ya ce bayanan sun nuna cewa a ma’aunin shekara bi-da-bi, hauhawar farashi a Nijeriya ya kasance da ƙarin kashi 9.79%, idan an kwatanta da kashi 21.91% da aka samu a Fabrairun 2023.

NBS ta ce, “Wannan na nuna cewa hauhawar farashin a matakin shekara bi-da-bi ya ƙaru a Fabrairun 2024, idan aka kwatanta da irin wannan watan a shekarar da ta gabata (wato, Fabrairun 2023)”.

Haka nan kuma, hauhawar farashin kayan abinci a Fabrairu ya kasance 37.92% a matakin shekara bi-da-bi.

Wannan ya kasance da ƙarin kashi 13.57% idan an kwatanta da yadda aka gani a Fabrairun 2023 (24.35%), a cewar rahoton.

Tun a baya, ƙaruwar tsadar rayuwa ta haifar da zanga-zanga a wasu yankunan ƙasar. Sai dai kuma, gwamnatin Nijeriya ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za ta magance waɗannan matsaloli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *