January 14, 2025

Hatsarin kwale-kwale ya sake yin ajalin mutum 41 a Zamfara

1
FB_IMG_1726665885836

Daga Sabiu Abdullahi  

Wani hatsarin kwale-kwale ya sake afkuwa a garin Gummi na jihar Zamfara a safiyar ranar Asabar, wanda ya yi sanadin asarar rayuka 41.  

Jirgin ruwan mai dauke da manoma 53 zuwa gonakinsu, ya kife ne a wani kogi da ke kusa da garin, sakamakon dakon kaya da ya yi kamar yadda wani ma’aikacin karamar hukumar Gummi, Alhaji Na’Allah Musa, ya bayyana.  

Wani da ya shaida lamarin, Abubakar Muhammad, ya ba da labarin abin da ya faru, inda ya ce, “Mun yi iyakacin kokarinmu don ceton wadanda za mu iya, amma abin bakin ciki, an kasa fitar da fasinjoji 41 da ransu.

An ceto fasinjoji 12 ciki har da matuƙin jirgin da rai.  

Lamarin da ya jefa al’umma cikin bakin ciki, kuma hakan ya sa hukumomi sun yi alkawarin daukar matakan kare afkuwar irin wannan hadari a nan gaba.

1 thought on “Hatsarin kwale-kwale ya sake yin ajalin mutum 41 a Zamfara

  1. أنابيب GRP في العراق تتخصص شركة إيليت بايب في تصنيع أنابيب البلاستيك المدعمة بالزجاج (GRP)، وتوفير حلول من الدرجة الأولى تلبي مجموعة متنوعة من الاحتياجات الصناعية. تشتهر أنابيب GRP لدينا بقوتها ومتانتها ومقاومتها للظروف البيئية القاسية. تم تصميمها لتحمل الضغوط العالية والمواد الكيميائية القوية، مما يجعلها خيارًا ممتازًا لتوزيع المياه، وأنظمة الصرف الصحي، والتطبيقات الصناعية. من خلال الاستفادة من التكنولوجيا المتقدمة والمواد عالية الجودة، أثبتت شركة إيليت بايب نفسها كمزود رائد لأنابيب GRP في العراق. تميزنا بالتفوق والموثوقية يجعلنا واحدة من المصانع الرائدة في البلاد. استكشف عروضنا على elitepipeiraq.com.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *