December 7, 2025

Hanyoyin da za ku bi wajen kiyaye asusunku na banki daga sharrin ƴan damfara

images (7) (24)

Daga Sabiu Abdullahi

Da yake yanzu zamani ne na hada-hadar banki ta yadda kusan komai da ya shafi harƙar kuɗi sai an haɗa da banki, haka ne ya sa wasu ja’iran mutane suka buɗe harƙar damfarar mutane ta hanyar satar bayanan da ke da alaƙa da bankin da mutum ke hidima da shi.

Mutane da yawa sukan yi rashin sa’a wajen faɗawa mummunan tarkon irin waɗannan mutanen.

Wasu mutanen, akan damfare su maƙudan kuɗaɗe, yayin da wasu kuma, kuɗin bai taka kara ya karya ba.

Akwai wanda kuma idan irin waɗannan ƴan damfara suka cuce shi, hakan zai zama sanadiyyar ƙaryewar tattalin arzikin rayuwarsa ke nan—zai iya shiga mummunan hali.

Wasu kuma, ƴan kasuwa ne, da zarar an damfare su, kasuwarsu ta kare ke nan.

Sau da dama, mutanen da ake damfara ba laifinsu ba ne. Ba su sani ba ne. Za su iya barin wasu bayanansu (kamar lambar jikin katin cire kuɗi, wato “ATM card”) saboda rashin sani. Wasu kuma zalama ce ke sakawa a damfare su.

Saboda haka, wannan dalilin ne ya sa muka ga ya dace mu zayyano wa jama’a irin matakan da za su ɗauka wajen tseratar da kansu daga sharrin irin waɗannan mutane masu damfara.

Ga wasu daga cikin matakan:

1. Kar mutum ya taɓa yarda ya tura lambar “activation code” ɗin manhajar bankinsa (mobile app) zuwa ga kowa, ko a waya, ko ta saƙon SMS, ko imel. Don haka a lura sosai.

2. Kar ka taɓa yarda ka bayyana lambar jikin katin cire kuɗinka (wato ATM card), lambar sirri ta zango ɗaya (OTP) da kuma lambobinka na sirri kamar “password” da “pin” ga kowa, ko da kuwa wanda yake buƙatar ka tura masa ya ce maka shi ma’aikacin bankinka ne.

3. Ka guji shiga “link” ko “attachment” ɗin da ba shi da tushe, sannan ya yi kama da na ƴan damfara. A kuma guji sauke manhaja daga shafin intanet marar tsaro ko marar ingantaccen tushe.

4. Kar ka amince da duk wani kiran waya, ko saƙon imel ko SMS da za a yi maka, ana maka tambayoyi game da asusunka na banki. Kar ka ba da bayani ko kaɗan ga irin waɗannan mutanen. Ƴan damfara ne.

5. Ka riƙa sabunta “operating system” ɗin wayarki tare da manhajar hada-hadar bankinka (wato mobile app).

6. Ka guji haɗa wayarka da duk wata manhajar “wifi” marar tsaro (ko kuma wacce ba ka san mai ita ba) da nufin neman shan data a banza.

7. Jama’a su sani cewa banki ba sa kiran mutum. Sai dai kai ka je da kanka idan kana da wata matsala. Saboda haka duk wanda ya kira ka, ya ce maka daga bankinka ne, to ka tabbata wannan ɗan damfara ne—kar ka faɗa masa komai game da kanka.

A kiyaye saboda guje wa da-na-sani!

3 thoughts on “Hanyoyin da za ku bi wajen kiyaye asusunku na banki daga sharrin ƴan damfara

Comments are closed.