April 18, 2025

Hamas Ta Saki Karin Mutum Uku, Isra’ila Na Shirin Sakin Falasɗinawa 600

adac7ed5-0237-4282-809e-813beeaf9f13.png.webp

Hamas ta saki karin mutum uku daga cikin fursunonin da aka shirya sakin yau Asabar, bayan rattaba hannu a takardu tsakaninta da wakiliyar ƙungiyar Red Cross.

Cikin waɗanda aka saki har da Eliya Cohen, mai shekara 27, wanda shi ne na farko da aka fara sakin. Sauran biyun kuwa su ne Omer Shem Tov, mai shekara 22, da Omer Wenkert, mai shekara 23. Hamas ta kama su ne a lokacin bikin waƙe-waƙen Nova da aka gudanar ranar 7 ga Oktoba, 2023. A yau aka mika su ga ƙungiyar Red Cross a garin Nuseirat, da ke tsakiyar Zirin Gaza.

Baya ga haka, an shirya sakin Bayahude na huɗu, Hisham al-Sayed, wanda Hamas ta kama tun 2015 bayan da ya tsallaka zuwa Gaza shi kaɗai. Ana sa ran za a sake shi daga baya a yau ba tare da wata gangamin jama’a ba.

A gefe guda, ana tsammanin Isra’ila za ta saki Falasɗinawa fiye da 600 daga cikin waɗanda take tsare da su a gidajen yari, a madadin Yahudawa huɗu da Hamas ke saki yau.

1 thought on “Hamas Ta Saki Karin Mutum Uku, Isra’ila Na Shirin Sakin Falasɗinawa 600

Comments are closed.