March 28, 2025

Hamas: Babu Mafita Ga Isra’ilawa Sai Ta Hanyar Sulhu

images-2025-02-15T104428.275.jpeg

A wata sanarwa da ta fitar a yau, Hamas ta ce sakin Isra’ilawan da ta yi ya nuna cewa babu wata hanya da za su kuɓuta, sai ta hanyar sulhu da aiwatar da sharuɗan yarjejeniyar tsagaita wuta.

Ƙungiyar ta kuma jaddada cewa: “Muna faɗa wa duniya cewa babu wata ƙaura, sai ta Birnin Ƙudus,” a matsayin martani ga shawarar Shugaban Amurka, Donald Trump, na kwashe al’ummar Gaza daga yankin zuwa ƙasashe makwabta.

A ‘yan kwanakin nan, an samu rudani kan ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta, bayan da Hamas ta yi barazanar dakatar da sakin Isra’ilawan, tana zargin Isra’ila da karya yarjejeniyar—a zargi da Isra’ila ta musanta.

1 thought on “Hamas: Babu Mafita Ga Isra’ilawa Sai Ta Hanyar Sulhu

  1. I think tthis iss among thhe mosst importqnt info foor me.
    Andd i amm glad readcing yourr article. But should reark on somee general things,
    Thee web siute sttyle iss wonderful, the articles iis really great : D.
    Goood job, cheers

Comments are closed.