Hamas ba ƴan ta’adda ba ne—Erdogan
Daga Sabiu Abdullahi
Shugaban Turkiyya Tayyip Erdogan ya bayyana a ranar Laraba cewa kungiyar Falasdinawa ta Hamas ba kungiyar ta’addanci ba ce.
Da yake jawabi a gaban ‘yan majalisa daga jam’iyyarsa ta AK mai mulki, Erdogan ya bayyana kungiyar Hamas a matsayin kungiyar ‘yantar da jama’a da ke fafutukar kare filayen Falasdinu da jama’arsu.
“Hamas ba kungiyar ta’addanci ba ce; kungiyar ‘yantar da jama’a ce, Mujahidai. Tana yaƙin kare ƙasashenta da mutanenta ne,” in ji Erdogan, yana amfani da kalmar Larabci da ke nuna masu fafutukar kare akidarsu.
Wannan furucin ya haifar da ce-ce-ku-ce, musamman tsakanin ƙasashen Turawa.