February 16, 2025

Hadaddiyar Daular Larabawa ta dawo ba wa ‘yan Najeriya biza

1
Tinubu-and-UAE-president.png

Daga Sabiu Abdullahi

Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta dage takunkumin da ta sanya wa ‘yan Najeriya na ba su biza, wanda zai fara aiki nan take.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a Mohammed Idris ne ya sanar da hakan bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya da shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a yau Litinin.

A cewar Idris, gwamnatin tarayya da hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawa sun cimma matsaya na janye dokar hana zirga-zirga da aka sanya wa ‘yan Najeriya.

Sakamakon haka, masu fasfo na Najeriya a yanzu za su iya zuwa UAE ba tare da wata tsangwama ba.

“An cimma yarjejeniyar, kuma daga yau masu dauke da fasfo din Najeriya da ke da niyyar tafiya UAE za su iya yin hakan,” in ji Idris. 

“Za a bayar da cikakkun bayanai nan gaba a yau idan muka fitar da sanarwa.”

Wannan lamari dai na zuwa ne bayan takaddamar diflomasiyya da dama da ta kai har Hadaddiyar Daular Larabawa ta kakaba wa Najeriya takunkumin shiga kasar shekaru biyu da suka gabata.

Wani bangare na haramcin ya biyo bayan gazawar da babban bankin Najeriya ya yi na mikawa kasar kudaden shiga da aka kiyasta kimanin dala miliyan 85, lamarin da ya sa kamfanin jiragen sama na Emirates na Dubai ya dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa Najeriya.

Sai dai kuma bayan wasu tarurrukan da ta yi da gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa, Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa nan ba da jimawa ba za a dage dokar hana shiga kasar.

A watan Yuni ne gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa ta biya kashi 98 na dala miliyan 850 da kasar UAE ke bin ta.

1 thought on “Hadaddiyar Daular Larabawa ta dawo ba wa ‘yan Najeriya biza

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *