January 15, 2025

Gwarzon damben Boxing na duniya ya sha da ƙyar a hannun sabon shiga ɗan ƙasar Kamaru

0
IMG-20231029-WA0009.jpg

Daga Katib AbdulHayyi

Gwarzon ajin masu nauyi na damben Boxing na Duniya, Tyson Fury, ya sha da ƙyar a hannun Francis Ngannou ɗan ƙasar Kamaru a damben Boxing na farko da Francis ɗin ya taɓa yi a matakin ƙwarewa.

Damben da ya gudana a daren jiya a birnin Riyad na Saudiyya, za a iya cewa shi ne dambe mafi samun halartar sanannun mutane, musamman na ɓangaren wasannin motsa jiki a baya-bayan nan.

Daga zakarun ƙwallon ƙafa an samu halartar Cristiano Ronaldo, Rio Ferdinand da Samuel Eto’o.

Daga ɓangaren masu wasan faɗa kuma tsohon gwarzon ajin tsakiya, Israel Adesanya; tsohon gwarzon ajin Welterweight, Kamaru Usman; tsohon gwarzon azuzuwan ajin marasa nauyi da na flyweight, Conor McGregor, mai riƙe kambunan boxin har uku; Alexander Usyk wanda yake ta hanƙoron samun damar karawa da Fury da wasu da ba za a iya ambatowa duka ba.

Francis Ngannou tsohon gwarzon faɗa na duniya ne a aji mafi nauyi ƙarƙashin UFC, kafin ya raba gari da kungiyar a shekarar da ta gabata kuma ya ajiye kambunsa ba tare da shan kaye ba.

Rabuwar ta faru ne saboda dalilai da dama, daga ciki har da batun hana shi gwada sa’arsa a fannin Boxing da UFC ta yi.

Masu bibiya a duk faɗin duniya sun bayyana al’ajabi da ganin yadda aka gwabza har tirmi goma ba tare da Gwarzon duniya Tyson Fury ɗan ƙasar Ingila ya yi wa Francis bugun kwaf ɗaya ba, sai ma Francis ɗin ne ya kusa yi masa a turmi na uku. Sai dai Furyn ya tsallake rijiya da baya.

An tashi ba tare da kaye ba, sai dai hukuncin alƙalai ya tabbatar da nasara ga Tyson Fury, yayin da suka bayyana cewa ya fi Francis da ɗigo ɗaya tak.

Sai dai mutane da dama sun nuna sun nuna rashin amincewarsu da sakamakon, ciki har da abokin hamayyar Fury z Alexander Usyk, Mike Tyson, Israel Adesanya, Daniel Comier, Jamain Sterling, Joe Rogan, da sauran ɗaruruwan sannanu a harkar dambe da faɗace-faɗace.

Akwai yiwuwar a sake shirya wannan dambe a nan gaba don a warware zare da abawa.

Kimanin watanni huɗu da suka wuce Ngannou ya ɗauki Mike Tyson a matsayin mai yi masa horo don ya kimtsa shi a shirin da yake na ɓarjewa da Tyson Fury. Mike Tyson yana ɗaya cikin mutanen da duniyar damben Boxing ba ta taɓa yin irinsu ba a tarihi.

A wannan dambe da aka gwabza, Francis da Tyson kowannensu zai samu dalar Amurka miliyan goma, kimanin naira biliyan bakwai da miliyan dubu ɗari tara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *