Gwamnonin PDP sun yi ƙira ga Tinubu da APC su yi murabus saboda matsalolin Najeriya
Daga Sabiu Abdullahi
Gwamnonin da aka zaba a karkashin tutar jam’iyyar adawa ta PDP, sun ƙara matsa ƙaimi ga shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki, inda suka bukaci su sauka daga mulki idan har ba za su iya samar da mafita mai dorewa ga kalubalen da Najeriya ke fuskanta ba.
Wannan kiran dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da fama da wahalhalun rayuwa, lamarin da ya sa gwamnoni ‘yan adawar suka bayyana cewa a karshe dai alhaki ya rataya ne a wuyan shugabannin kasar.
A cikin wata sanarwa da kungiyar gwamnonin PDP (PDP-GF) ta fitar a baya-bayan nan, gwamnonin sun bayyana cewa halin da ‘yan Najeriya ke ciki ya wuce na kabilanci, addini, ko siyasa.
Sun nanata cewa APC ta karbi mulki ne da hurumin rage radadin da Najeriya ke ciki, ba wai ta ta’azzara su ta hanyar zargi ko farfaganda ba.
A cewar babban daraktan ƙungiyar gwamnonin, Hon. CID Maduabum, Shugaba Tinubu yana da hakki a matsayin “babban jami’in zartarwa na kasa,” yana mai jaddada matsayinsa na shugaban kasa da kuma jagoran jam’iyya mai mulki.